Yadda ake amfani da “Has”, “Have”, da “Had”, a cikin jimla (Sentence)

Hello Everyone! in this topic, I’m going to explain how to use “Has”, “Have”, and “Had, in English

Barkan ku dai. A yau zamu yi bayani ne akan yadda za a yi amfani da kalmar “Had”, “Has” da “Had” a turanci.

Amma kafin mu fara, yana da kyau ku daina wasu ayyukan da za su sa ku shagala, domin mai koyo ba zai iya ganewa ba, matukar ba mai da hankali ga abin da ka ke koya ba.

So, let’s begin with “Has”; = Tom, bari mu fara da “Has”

1. HAS

Has” is a singular anomalous verb.

Ma’ana: Ita “has” tana tafiya ne da tilo (singular), duk abun da aka ce tilo ana nufin abu ne guda daya, shi ne ake kira da (Singular) a turanci.

Has” always goes with 3rd person, singular pronouns or singular subject. Example: He, She, It

Ma’ana: Ita “has” tana tafiya da tilo (singular) na wakilin suna (abun da ake magana akansa). Misali Shi, Ita ko abu marar rai It, sannan kuma ana amfani da ita ga ko wanne irin suna ne wanda yake tilo, za’a iya amfani da “Has

Here is the Example of Has in sentence.

 • The plant Has dried = Tsirran har ya bushe.
 • She Has gone home = Ta rigada ta tafi gida.
 • He Has just returned now = Ya rigada ya dawo yanzu.

2. HAVE

Have” is a plural form of “has”.

Note: In this case, “have” always goes with plural nouns.

Abin Lura: “Have” tana tafiya da jam’i ne ba tilo ba, kuma jam’in ya hadarda, mutane, ko dabbobi harma da wasu abubuwa, amma su kasance ba tilo ba sai dai jam’i daga biyu har zuwa sama. Toh, shi ne ake amfani da “Have

Here is the example of Have in sentence.

 • They have gone = Sun rigada sun tafi.
 • I have plenty cars = Ina da motoci masu yawa.
 • We don’t have much time = Ba mu da lokaci da yawa.
 • You have two minutes left = Mintina biyu suka rage ma.
 • I have told you = Na rigada na fada ma.

Please, Don’t be confused because I used “I” with “have“. The rule is an exception. Remember, in almost every grammar rules, we have exceptions. Although “I” is singular, it always goes with “have”. eg. I Have a car. I Have money. etc.

Saboda haka “I” tana tafiya da “Have” saboda dokar turanci bata aiki a kanta, shiyasa na baku misalin cewar za’a iya cewar, I have a car = Ina da mota, ko I have Money = Ina da kudi. da sauransu.

3. HAD

“Had” is used as past participle.

Remember, “have” and “has” are used in Present Perfect Tense. While “had” is used in past perfect tense

Misali: Ita “had” ana amfani da ita akan aikin da ya wuce a baya (past tense). Ita kuma “has” da “have” ana amfani da su a present tense.

Here is the examples of Had in sentence.

 • I had a car = Da ina da mota.
 • I had money = Da ina da kudi

Like i told you, “Had” as the past tense of “has” and “have” can go with either singular or plural nouns.

Eg.

 • I had a car.
 • She had a car.
 • He had a car.
 • We had a car.
 • You had a car

These sentences indicate that the subjects possessed a car in the past

Wadannan jimloli suna bada labari ne, da can a baya suna da mota, amma yanzu ba lallai sun da motar ba, saboda sun bayarda labari abun da ya faru a baya.

Wannan shine bambancin

In nutshell “Has” is singular “Have” is plural “Had” is past tense of “has” and “have”.

A nan ne muka kawo karshen wannan darasi, kuma muna fatan kun amfana da abin da muka kawo. Sannan za mu ci gaba da kawo muku wasu muhimman darussa da za su taimaka muku koyon Turanci cikin sauki.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *